Kungiyar kasashen Afrika tace ta kashe akalla uku daga cikin yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab ta kasar Somaliya guda takwas da suka kaiwa daya daga cikin sansaninta a birnin Mogadishu hari, ke nan an kashe mutane goma sha hudu.
Mai magana da yawun ofishin kungiyar AU da ake cewa AMISOM a takice, Kanal Ali Aden Hamoud ya fadawa Muryar Amirka cewa, a ranar Alhamis aka kashe sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU guda biyar da wani dan kwangila a harin da aka kaiwa daya daga cikin sansanin kungiyar.
Kanal Ali Aden Hamoud yace, yanzu haka ana gudanar da bincike domin tantance yadda aka yi har yan yakin sa kan cikin umifam na sojojin Somaliya suka kutsa sansanin na Halane dake kusa da filin saukar jiragen saman birnin Mogadishu.
A lokacinda tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai hain, kungiyar Al Shabab tace harin ya auna bikin Kirisimeti da ake yi a sansanin.
Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon yayi Allah wadai da harin, kuma ya jaddada cewa Majalisar Dinkin Duniya zata ci gaa da goyon bayan gwamnatin Somaliya.