Hukumomin jahar Naija a arewacin Najeriya sun yi bikin ranar ciwon sukari ta duniya
WASHINGTON, DC —
A jahar Naija da ke arewacin Najeriya an gudanar da bikin ranar duniya ta ciwon sukari kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta yi tanadi kowace shekara a ranar goma sha hudu ga watan goma sha daya domin maida hankali kan masu wannan cuta da kuma kara fadakar da jama'a a kan cutar. Wata kididdigar da aka gudanar ta nuna cewa a duniya mutane sama da miliyan dari uku da saba’in da daya ne ke shan wahalar wannan ciwo na sukari. Dakta Idris Muhammad shi ne shugaban kungiyar masu fama da cutar a jahar Naija, a tattaunawar su da wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari, Dakta Idris Muhammad ya ce wannan rana ta na da muhimmancin gaske wajen tunatarwa da kuma fadakarwa.