Kafofin yada labarun kasar Sudan sunce wani jirgin ruwa dankare da yan gudun hijira, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudi Arabiya ya nutse. Mutane dari da casa'in da bakwai sun mutu.
Kamfanin dilancin labarun Sudan yace an ceci mutane uku daga cikin jirgin ruwan, wanda har yanzu hukumomi ke neman ko wasu sun tsira. Kamfanin dilancin labarun yace jirgin ya kama wuta.
Rahoton bai fadi ko yan wace kasa ce ke cikin jirgin ba, to amma sun fito ne daga kasashe makwaptan Sudan.
A duk shekara dubban yan gudun hijirar Afrika ne ke tsaklaka mashigin Aden domin gujewa talauci da fatara da kuma tarzoma. Yawancin yan gudun hijira su kan yi wannan tafiya ne cikin jiragen ruwan yan smogal da aka cika fiye da kima wadanda a wasu lokutan aka dankara musu duka sa'ana a jefa su cikin teku.
An dauka hanyar teku ta mashigin Aden da tekun baharmaliya, zama mafi hatsari a duk fadin duniya.