Ofishin Majalisar Dinkin Duniy dake Sudan a yankin Darfur yace ya fara shirin kwance damar tsoffin mayaka kamar dari hudu, daga duka sassan, ‘yan tawaye, da gwamnati a yakin da ya dauki lokaci mai tsawo.
Majalisar tace jiya litinin ce ta fra aiwatara da shirin a El Fasher dake arewacin Darfur, kuma ya kunshi tsoffin sojoji gwamnatin da kuma ‘yan tawaye.
Wadanda suka samu shiga cikin shirin za’a tanatancesu, da kuma auna lafiyarsu ta ko wani fanni. Shirin zai hada da sake yi musu tarbiya domin komawa cikin al’uma, koya musu sana’o’I d a kuma basu alawus na kudi domin taimaka musu su sami sukunin zama.
Wan nan sabon shiri da majalisar ta fara a arewacin Darfur, yazo ne wata biyu bayan ta kaddamar da irin wan nan shiri a kudancin Darfur, inda tayi aiki da tsoffin sojoji 1,100.
‘Yan tawaye a Darfur sun saba makamai ne a 2003 domin tunkarar gwamnatin kasar dake Khartoum sabo da zargin tayi watsi da yankin.