Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace barazanar da shugaban Libya Moammar Gadhafi yayi kan kungiyar tsaro ta NATO, ba zai hana kungiyar ci gaba da matakai da take dauka kan kasar ba.
Asabar din nan ce madam Clinton tayi wan nan furuci lokacinda ta kai ziyara Spain, ko Andalusiya.
A cikin sakon da aka yadawa dubban magoya bayansa da suka hallara a wani dandali a fadar kasar jiya jumma’a, shugaba Gadhafin dake cikin tsaka mai wuya, yayi barazanar cewa NATO zata fuskanci sakamako mara dadi, muddin bata kawo karshen farmaki ta sama da take kaiwa kan Libya.
Birnin Tripoli ne cibiyar i da kanal Gadhafi ya saura da iko cikin kasar, da ahalin yanzu yaki ya dai-daita, kuma nan ne sojojin taron dangi suke ta kaddamar da hare hare kan sojoji masu biyayya ga gwamnati.
Ranar litinin ce kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuffuka ta bada sommacin a kama kanal Gadhafi da dansa Saiful Islam, da shugaban hukumar leken asirin kasar kan zargin kitsa hare hare d a suka kai ga halaka farar hula a cikin watanni da aka yi ana bore a kasar.