Yan tawayen kasar Libya sun kai farmaki kan tsaunukan dake kudu maso yammacin Tripoli babban birnin kasar a yunkurin kutsawa kurkusa da Tripoli inda shugaban kasar Moammar Gadhafi yake da karfin iko. Yan tawayen sun yi amfani da manyan makamai yau Laraba wajen kutsawa yankin al-Qawalish wani wuri dake karkashin ikon gwamnati kusa da Tripoli. Shaidu sun ce sun ji karar jiragen yakin NATO suna shawagi. Wannan fadan ya biyo bayan kashe ‘yan tawaye 11 da aka yi a wata arangama tsakanin dakarun dake goyon bayan gwamnati da birnin Misrata dake karkashin ikon ‘yan tawaye. Ma’aikatan jinya da kuma ‘yan tawayen sun ce an kashe mutanen ne tsakanin ranar Litinin da Talata bayanda dakarun dake biyayya da shugaba Moammar Gadhafi suka kai farmaki a wajen Misrata dake kimanin tazarar kilomita 200 da gabashin Tripoli. Bisa ga cewarsu, sama da ‘yan tawaye 40 suka jikkata.
Yan tawayen kasar Libya sun kai farmaki kan tsaunukan dake kudu maso yammacin Tripoli babban birnin kasar a yunkurin kutsawa kurkusa da Tripoli inda shugaban kasar Moammar Gadhafi yake da karfin iko.