Yan gwaggwarmaryar kasar Syria sun ce dakarun gwamnati sun harbe suka raunata a kalla mutane shida a wani farmaki da suka kai a kauyuka da dama dake arewa maso gabashin kasar a hari na baya bayan nan kan masu zanga zangar kin jinin gwamnati. Yan gwaggwarmayar sun ce dakarun kasar Syria sun kai harin ne a Kfar Roumah da kuma wadansu kauyuka a lardin Idlib yau Litinin. A wani wuri kuma, mai sawa kungiyar kare hakin bil’adama ido yace sojoji sun kama sama da mutane 20 a sumamen da suka kai kan gidaje a birnin Hama wata cibiyar nuna kin jinin mulki shekaru goma sha daya na gwamnatin shugaba Bashar Assad. Mai sa idon yace mazauna birnin sun kona tayoyi suka kuma girke duwatsu kan tituna domin hana dakarun walwala. Dubun dubatan mutane sun shiga zanga zangar kin jinin gwamnatin a Hama ranar jumma’a, a daya daga cikin zanga zanga mafi girma da aka gudanar a kasar Syria tunda aka fara nuna kin jinin gwamnatin a watan Maris. Mr. Assad ya kori gwamnan lardin Hama kwana daya bayan zanga zangar. Yan gwaggwarmaya da kuma mazauna lardin sun ce jami’an tsaro sun kashe masu zanga zangar kin jinin gwamnati guda biyu jiya Lahadi a Damascus babban birnin kasar. Suka ce an kashe mutanen ne a Hajar Aswad, wurin da aka saba gudanar da zanga zangar kin jinin Assad.