Gwamanatin jihar Legas da ke kudu maso yammcin Najeriya ta ce mutum dubu 161, 040 cikin mutum 404, 414 da aka yi wa allurer riga-kafin cutar coronavirus a karon farko, ba su koma sun karbi allurar ta biyu ba.
Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana hakan inda ya yi kira ga al’umar jihar da su yi taka-tsantsan domin kaucewa cutar wacce ke kara yaduwa a karo na uku a jihar, wacce ta fi yawan masu kamuwa da cutar a Najeriya.
Hukumomin jihar sun ce cikin kwana shida da suka gabata, mutum 30 ne suka mutu.
“Karin adadin wadanda ke mutuwa sanadiyyar cutar ta coronavirus da aka gani cikin makon da ya wuce, ya sa mu cikin yanayi na damuwa yayin da cutar ta kara tasowa a karo na uku.” In ji Sanwo-Olu.
A cewar gwamnan, an ga karin masu kamuwa da cutar ninkin-ba-ninkin a jihar ta Legas, abin da ya yi sanadin samun mutum 4,300 da cutar ta harba a watan Yuli kadai, yayin da aka kwantar da mutum 352 a wuraren da aka ware domin masu cutar.
A cewar Sanwo-Olu, jihar ta Legas na gab da samun allurar Moderna da aka ba gwamnatin tarayya.
“Ina kira ga mazauna Legas, wadanda ba su karbi allurar ba ko a karon farko, da su fita su karba, saboda za a yi masu allurar ne sau daya tak.”
Sai dai ya ce wadanda suka karbi allurar Astrazeneca kada su karbi ta Moderna domin ba a hada alluran biyu.
“Har yanzu muna sai rai da samun karin allurar ta Astrazeneca kafin karewar watan Agusta domin yi wa wadanda suka karbi allurar daya saboda su karbi ta biyun.”