Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Gwamnati Ta Ba Da Shawara A Jingine Hawan Sallah


Hawan Fanisau (Facebook/ Masarautar Kano/ Kamfa Photography)
Hawan Fanisau (Facebook/ Masarautar Kano/ Kamfa Photography)

A ranar 8 ga watan Yuli cibiyar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya, ta sanar da bullar sabuwar cutar ta COVID-19 nau’in Delta, wacce masana suka ce tana da saurin yaduwa.

Kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar coronavirus, ya nemi jihohi shida hade da babban birnin tarayya na Abuja, da su zauna cikin shirin kar-ta-kwana saboda yaduwar cutar coronavirus.

Kazalila kwamitin ya ba da shawarar a jingine bukukuwan hawan sallah da aka saba yi.

Cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin, Boss Mustapha ya fitar kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito, Sakataren gwamnatin tarayyan ya zayyana jihohin Legas, Oyo, Rivers, Kaduna, Kano da Filato a matsayin wadanda aka yi masu garagdin su zauna cikin shiri.

Kwamitin har ila yau cikin sanarwar wacce aka fitar a ranar Lahadi, ya nemi sauran jihohin kasar da su kara tsaurara matakai yayin da Najeriyar ke shirin fuskantar barazanar tashin cutar a karo na uku.

Gwamnati har ila yau ta yi kira ga Musulmi da ke shirye-shiryen bukukuwan sallah, da su yi takatsatsan wajen yin shagulgulan sallar, inda ta nemi da a rarraba gudanar da sallar Idi zuwa wasu masallatan Juma’a.

A ranar 8 ga watan Yuli cibiyar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya, ta sanar da bullar sabuwar cutar ta COVID-19 nau’in Delta, wacce masana suka ce ta na da saurin yaduwa.

Izuwa ranar 18 ga watan Yuli, mutum 169, 329 aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya yayin da 2,126 suka mutu.

A watan Fabrairun bara, Najeriya ta fara samun bullar cutar ta COVID-19.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG