Bayan dawowar shugaba Buhari a karo na biyu a shekarar 2019, gwamnatin tarayya ta sha alwashin fitar da ‘yan Najeriya Miliyan 100 daga tafarkin talauci kafin karewar wa’adin karo na 2 a 2023.
Hakan ne ya sanya gwamnati fito da tsare-tsaren tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu damar bullo da shirye-shiryen horas da matasa sana’o’i daban-daban, tare da fitar da biliyoyin naira domin cimma wannan buri.
Sai dai a sakonta ga taron bita na masu ruwa da tsaki a hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu ta Najeriya wato SMEDAN, wanda aka kammala a karshen mako a Kano, minista na ma’aikatar ciniki da harkokin Zuba Jari Hajiya Maryam Katagum ta ce, annobar Coronavirus ta mayar da hannun agogo baya ga wannan aniya ta gwamnati.
Sai dai Darakta Janar na hukumar SMEDAN mai kula da lamuran kananan da matsakaitan masana’antu Dr. Dikko Umaru Raddaya ya ce duk da wannan kalubale kwalliya na biyan kudin sabulu.
Alkaluman baya-bayan nan da hukumar NBS mai kidddigar al’amura a Najeriya ta fitar, sun ce talauci na kara zurfi a tsakanin talakawan Najeriya saboda matsaloli da dama ciki har da karancin ayyukan yi.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari: