Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Bullar Nau’in Delta Na Cutar Coronavirus A Najeriya - NCDC


Shugaban Najeriya, Shugaban Buhari lokacin da aka yi masa allurar rigakafin COVID-19
Shugaban Najeriya, Shugaban Buhari lokacin da aka yi masa allurar rigakafin COVID-19

Hukumar Lafiya ta WHO, ta ayyana wannan nau’in cuta ta COVID-19 a matsayin abin damuwa, lura da yadda take saurin yaduwa.

Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya, ta ce ta gano sabon nau’in Delta na cutar coronavirus a kasar.

“Hukumar NCDC ta gano, ta kuma tabbatar da bullar nau’in SARS-CoV2 Delta, wanda aka samu a jikin wani matafiyi da ya shiga Najeriya.” Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Alhamis ta ce.

A cewar hukumar, an gano matafiyin na dauke da nau’in cutar ne bayan gwajin da aka yi masa wanda akan yi wa fasinjoji daga kasashen waje.

Hukumar Lafiya ta WHO, ta ayyana wannan nau’in cuta ta COVID-19 a matsayin abin damuwa, lura da yadda take saurin yaduwa.

Tuni an riga an gano bullar cutar a kasashe sama da 90, ana kuma fargabar za ta yadu zuwa wasu kasashen a cewar NCDC.

“Ana kan gudanar da bincike domin a fahimici irin tasirin wannan cuta akan allurar rigakafin da ake da ita da sauran hanyoyin magance cutar,” a cewar NCDC.

NCDC ta ce, tana aiki tare da cibiyar binciken magunguna ta kasa (NIMR) da cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Afirka ta ACEGID, da zimmar ganin an kara fahimtar yadda wannan cuta ke hayayyafa.

Izuwa ranar Alhamis 8 ga watan Yuli, Najeriya na da mutum 168,110 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus sannan mutum 2,122 sun mutu a cewar NCDC.

XS
SM
MD
LG