Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 85 Sun Mutu Sannan Wasu 2, 510 Sun Murmure Daga Cutar Sankarau Cikin Watanni 4 A Jihar Yobe


Yobe, Nigeria
Yobe, Nigeria

Yayin hirarsa da manema labarai a birnin Damaturu, Kwamishinan Lafiya na yobe, Dr. Lawan Gana, ya musanta rahotannin dake yawo a kafafen sada zumunta game da zargin mutuwar mutane 200 a kananan hukumomin Potiskum da Nangere na jihar.

WASHINGTON DC - Gwamnatin Yobe ta bayyana cewar annobar sankarau ta hallaka mutane 85 a jihar, sannan mutum 2, 510 sun murmure bayan sun kamu da cutar tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun shekarar da muke ciki ta 2024.

Yayin hirarsa da manema labarai a birnin Damaturu, Kwamishinan Lafiya na yobe, Dr. Lawan Gana, ya musanta rahotannin dake yawo a kafafen sada zumunta game da zargin mutuwar mutane 200 a kananan hukumomin Potiskum da Nangere na jihar.

An ruwaito shi yana cewar, “game da batun sankarau, mutane 85 sun mutu kuma mutum 2, 510 sun murmure bayan da suka kamu da cutar.

Ina mai baku tabbacin cewar, gwamnati jihar Yobe tayi nasarar dakile lamarin, saidai muna bukatar gwamnatin tarayya ta bamu gudunmowar karin alluran rigakafi domin shawo kan annobar a fadin jihar”.

Ya kara da cewar, duk da cewar hadin gwiwar masana kwayoyin cuta da hukumar lafiya a matakin farko na jihar sun gudanar da zuzzurfan bincike domin tantance sahihncin wadancan rahtanni, an tabbatar da cewa babu kamshin gaskiya a cikinsu.

A cewarsa, “kafin mu kalubalnci rahotannin a matsayinmu na ma’aikatar lafiya, sai mun gudanar da namu bincike domin tantance gaskiya. Bayan da muka samu rahoton, sai muka umarci masana kwayoyin cutar dake jihar, karkashin kulawar darakta mai kula da lafiyar al’umma inda suka fara da tuntubar tawagogin jami’an lafiyar dake kananan hukumomin da ake zargin cutar ta hallaka mutane, saidai an samu babu wani zance mai kama da hakan”.

A cewar Dr. Lawan Gana, yanayin zafi na taimakawa wajen barkewar annobar, inda ya bukaci al’umma dasu tabbatar suna kwana a wurare masu wadatacciyar iskar tare da kai rahoton duk wata bakuwar cuta ga cibiyoyin kiwon lafiya akan lokaci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG