Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Mali Sun Kashe Wani Jigon Kungiyar IS Da Amurka Ke Nema Ruwa A Jallo


MALI-Sojoji
MALI-Sojoji

Sojojin kasar Mali sun kashe Abu Huzeifa, kwamandan kungiyar Da'ish a yammacin Afirka, a wani gagarumin farmaki da suka kai a yankin Menaka da ke arewacin kasar, a cewar sanarwar da hukumomin Malin suka karanta a gidan talabijin din kasar a ranar Litinin din nan.

WASHINGTPN, D. C. - An tabbatar da mutuwar Huzeifa a ranar Lahadin da ta gabata bayan wani samame da aka kai a yankin Indelimane, in ji su, amma ba su yi karin bayani a kai ba.

Shirin bayar da tukwici don tabbatar da adalci na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, na tayin tukwicin dala miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan Huzeifa, saboda zarginsa da aka da taka rawa a harin da aka kai a makwabciyarta Nijar a shekarar 2017, wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Amurka hudu da na Nijar hudu.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, hare-haren kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da IS sun yi sanadin mutuwar dubban mutane a kasashen Mali da Nijar, da kuma makwabciyarta Burkina Faso, lamarin da ya janyo rashin zaman lafiya a yankin Sahel na yammacin Afirka.

Ya zuwa watan Maris, matsalolin tsaro da na jinkai da aka dade ana fama da su ya raba sama da mutane miliyan uku da muhallansu a yankin, a cewar Kungiyar Kula da Hijira ta Duniya.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG