Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Yi Amfani da Kashin Dabbobi Mu Samo Ma Al'umma Wutar Lantarki -Gwamnan Neja


Gwamnan jihar Neja, Umar Bago
Gwamnan jihar Neja, Umar Bago

WASHINGTON DC - A wani yunkuri na bunkasa harkokin noma, tattalin arziki da rage radadin talauci a jihar Neja, gwamnatin jihar ta ce za ta yi amfani da kashin dabbobi ta samar wa al’ummar jihar wutar lantarki.

Gwamnan jihar, Umar Bago ne ya sha alwashin yin haka, da yake wata kebabbiyar hira da wakilin Muryar Amurka, Mohammed Hafiz Baballe, a birnin Washington DC a kasar Amurka, jim kadan bayan halartar wani taro da Cibiyar Bunkasa Zaman lafiya na Kasar Amurka ta shirya.

“Kashin wadannan dabbobi da muke da su. Wanda za mu fara tarawa a wuri daya, za mu yi amfani da shi mu samar da wutar lantarki da abun da za'a yi noma da shi,” in ji Gwamna Bago.

Ya kara da cewa sun cimma yarjejeniya da kamfanin Baer, Ranke da ma UNDP wurin samar da ilimin fasahar noma ga ‘yan karkara da ma duk manoma a fadin jihar.

Gwamnan ya ce bisa yadda aka kaddamar da irin wadannan shirye-shirye a baya, inda yawancin wadanda gwamnati ta basu turaktoci da taki suka sayar, wannan karon za'a canza salo ayi wa manoma aiki akan gonakinsu.

“Mun lura cewa gwamnatocin da suka shude tun daga farko, idan sun kawo wadannan turaktoci sun bayar, sayarwa ake yi. Saboda haka mun kafa kamfani da zai hada hannu da wadannan kamfanoni na kasar Amurka don su sa ido akan turaktocin da taki.

Talaka ya na so a yi masa noma, za'a je a gyara masa filinsa. A yi masa shukin abun da yake so ya shuka yadda ya kamata. Akwai inji kala-kala na kayan noma wanda zai nuna yadda ya kamata a yi irin wannan shukin da shi, saboda haka ba za'a raba wadannan injunan ba, za'a yi aiki da su ne,” in ji shi.

Da yake mayar da martini kan irin sukar da ‘yan Najeriya ke yi kan yadda gwamnonin suka halarci taron da ke neman mafita ga matsalolin tsaro da yankunan arema maso yamma da tsakiya ke fuskanta, ya ce “mun samu ilimi sosai na yadda za'a kasantar da zaman lafiya ga al’umma, har ma da dalilai da misalin abubuwan da ke jawo afkuwan irin wadannan munanan iftila’i. Saboda haka za mu koma da ilimin zaman lafiya.”

Za Mu Yi Amfani da Kashin Dabbobi Mu Samo Ma Al'umma Wutar Lantarki - Gwamnan Neja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG