Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsanancin Zafi Da Ambaliyar Ruwa Sun Kashe Mutane 11 A Indiya


India
India

A ranar Larabar nan ne Indiya ta yi fama da matsanancin yanayi da ya haifar da tsananin zafi da zabtarewar kasa da kuma ambaliyar ruwa.

Lamarin dai ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 11 a cikin wannan mako, ciki har da wata mata da 'ya'yanta mata uku da gocewar kasa ta binne da ransu a jihar arewa maso gabashin kasar, in ji jami'ai da kafofin yada labarai.

India
India

New Delhi, babban birnin kasar, ya gamu da zafi mafi tsananin a cikin shekaru shida a ranar Talata, inda asibitoci a birnin mai miliyan 20 suka ba da rahoton mutuwar akalla mutane biyar sakamakon tsananin zafi a wannan makon, in ji jaridar Times ta India.

Ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa sakamakon ruwan sama da ya ki tsayawa a jihar Assam da ke arewa maso gabashin kasar ya kashe akalla mutane shida da daren ranar Talata, in ji jami'ai. Wani jami’in hukumar kai daukin gaggawa a jihar, Siju Das, ya bayyana ta wayar tarho cewa, “Zabtarewar kasa ta binne wata mata da ‘ya’yanta mata uku da rai cikin dare.

“Gidan nasu na kan tudu ne, kuma nan take suka mutu da tsakar dare,” in ji shi, ya kuma kara da cewa an zakulo gawarwakinsu ne bayan wani samame na sa’o’i uku da jami’an ceto suka yi.

"Haka kuma wani yaro ‘dan shekara uku ya mutu.

Biliyoyin mutane a fadin Asiya na fama da matsanancin zafi a wannan bazarar, a wani al'amari da masana kimiya suka ce sauyin yanayi da ‘dan Adam ke haifarwa ne ya ta'azzara.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG