Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye Da Mutane 35 Sun Mutu A Gobarar Da Ta Tashi A Kuwait


Kuwaiti firefighters and security forces gather outside a building which was ingulfed by fire, in Kuwait City, on June 12, 2024.
Kuwaiti firefighters and security forces gather outside a building which was ingulfed by fire, in Kuwait City, on June 12, 2024.

Sama da mutane 35 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da wata gobara ta tashi a wani gini da ke dauke da kusan ma'aikata 'yan kasashen waje 200 a Kuwait, kamar yadda jami'ai suka bayyana a ranar Laraba.

Ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce mutane arba’in da uku ne suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi a yankin Mangaf da ke kudancin birnin Kuwait wanda ke da dimbin ma’aikata ‘yan ci-rani.

Mun samu rahoton gobara da karfe 6:00 na safe (0300 agogon GMT) a yankin Mangaf,” in ji Manjo Janar Eid Al-Owaihan, shugaban sashen tabbatar da laifuka na ma’aikatar cikin gidan kasar.

Gobara
Gobara

"Game da wadanda suka mutu a ginin da ke baya na, adadin ya zarce 35 ya zuwa yanzu."

Kuwaiti mai arzikin mai, tana da ma'aikata 'yan kasashen waje da dama, da yawa daga cikinsu daga kudu maso gabashin Asiya ne, kuma galibi suna aikin gine-gine ko kuma a masana'antu.

A cewar wata majiya daga babban ofishin hukumar kashe gobara, wadanda abin ya shafa sun shake ne da hayakin da ya tashi bayan gobarar ta tashi.

Tawagar masu bincike na aiki a wurin kuma sun gano gawarwaki uku kawo yanzu, in ji Owaihan.

Ba a bayyana asalin kasashen mutanen da abin ya shafa ba amma jakadan Indiya da aka tuntube shi, ya shaida wa AFP cewa yana asibiti don ziyartar wadanda suka tsira.

Ministan harkokin cikin gida Sheikh Fahd Al-Yousef ya bayyana cewa, an tsare mai ginin yayin da aka kaddamar da bincike.

“Za mu yi aiki don magance matsalar cunkoson ma’aikata da rashin kula,” in ji Ministan. "Za mu tsare mai gidan da gobarar ta tashi har sai an kammala matakan shari'a."

Gobarar dai na daya daga cikin mafi muni da ake gani a kasar Kuwait mai makwabtaka da Iraki da Saudiyya kuma tana kan kusan kashi bakwai cikin dari na arzikin man fetur na duniya.

A shekara ta 2009, mutane 57 ne suka mutu a lokacin da wata mata ‘yar kasar Kuwait, ta kona wani tanti a wajen wani bikin aure, lokacin da mijinta ya kara aure.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG