Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Da Ta Tashi Lokacin Gyaran Wani Gidan Rawa A Istanbul Ta Kashe Mutane 27


Istanbul, Turkey - Gobara
Istanbul, Turkey - Gobara

Wata gobara da ta tashi a wani gidan rawa da ke birnin Istanbul a lokacin da ake yin gyare-gyare a ranar Talata, ta kashe mutane akalla 27, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

WASHINGTON, D. C. - An kuma tsare mutane da dama da suka hada da manajojin gidan rawar domin amsa tambayoyi.

Istanbul - Gobara
Istanbul - Gobara

A cikin wata sanarwa da ofishin gwamnan Istanbul ya fitar, ya ce akalla mutum guda yana jinya a asibiti.

Gidan rawan Masquerade Nightclub, wanda aka rufe don gyarawa, yana ƙasa kuma karkashin benaye na wani gidajen zama mai hawa 16 a gundumar Besiktas da ke gefen Turai na birnin wanda Bosphorus ya raba. Daga baya an samu kashe wutar.

Gwamna Davut Gul ya shaidawa manema labarai a wurin da lamarin ya faru cewa, ana gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar, kuma ana kyautata zaton wadanda abin ya shafa masu aikin gyara ne a wajen.

‘Yan Sandan Istanbul, Turkey Afrilu 02, 2024
‘Yan Sandan Istanbul, Turkey Afrilu 02, 2024

Hukumomin kasar sun tsare mutane biyar domin yi musu tambayoyi da suka hada da manajojin gidan rawar da kuma mutum daya da ke kula da gyare-gyaren, in ji ministan shari’a Yilmaz Tunc.

Magajin garin Ekrem Imamoglu ya ce hukumomi na kuma duba daukacin ginin domin tantance lafiyarsa.

Ya ce an aike da jami’an kashe gobara da na likitoci da dama zuwa wurin.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG