Sanata Tahir Monguno, mai wakiltar Arewacin Jihar Borno, wanda shine shugaban Kwamitin kula da bangarorin Shari’a, ‘Yancin dan Adam da kuma Dokoki, ya maye gurbin Sanata Ali Ndume , mai wakiltar Kudancin Jihar Borno, a matsayin Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawan Najeriya.
Da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya bukaci a kada kuri’a akan batun ta hanyar amfani da murya, mambobin kwamitin kolin jam’iyyar APC a Majalisar Dattawan sun goyi bayan sauke Ndume daga kan kujerarsa.
Hakan na zuwa ne sakamakon sukar baya-bayan nan da Ndumen ya yiwa gwamnatin Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu.
Wata wasika da shugabancin apc na kasa ya aikewa kwamitin kolin jam’iyyar a Majalisar Dattawa, ta bukaci Ndume yayi murabus daga zama mamba a jam’iyyar tare da shiga duk jam’iyyar adawar daya zaba.
Wasikar na dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Sakatarenta Barista Ajibola Basiru.
Dandalin Mu Tattauna