Dubban mutane ne a kasar Kamaru suka yi jerin gwano a tsakiyar birnin Yaounde babban birnin kasar jiya asabar, domin numa adawa da kungiyar mayakan Boko Haram da kuma goyon bayan dakarun dake kokarin kawo karshen hare haren kungiyar.
Kamaru ta shiga sahun kasashen Najeriya da Chadi da kuma Nijar da suke iyaka da yankin da kungiyar Boko Haram tafi karfi, a wani shiri na hadin guiwa a yaki da kungiyar mai kaifin kishin Islama. Daya daga cikin wadanda suka shirya jerin gwanon, dan jarida Guibal Gatama, ya shaidawa Muryar Amurka cewa, jerin gwanon nuna goyon bayan ne ga miliyoyin mutanen da kungiyar Boko Haram ta jefa cikin halin kunci.
Kimanin mutane dubu dari da hamsin ne suka rasa matsugunansu a Najeriya, inda Boko Haram ke da karfi, yayinda kimanin dubu dari biyu kuma suka kaura daga Najeriya zuwa wadansu kasashe.
A hari na baya bayan nan, mayakan Boko Haram sun kashe ‘yan kasuwa da dama a wata kasuwa dake jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.
Majiyun jami’an tsaro sun ce harin da aka kai ranar Jumma’a shine na biyu a jerin manyan hare hare da aka kai cikin watanni biyar kan kasuwar Mainok, dake tazarar kilomita sittin da biyar da Maiduguri babban birnin jihar Borno.