Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Minista Ya Bai Wa ‘Yan Najeriya Tabbacin Kokarin Magance Tsadar Kayan Abinci


Kayan abinci
Kayan abinci

Alkaluman baya-bayan nan daga ofishin kididdiga na kasa sun nuna cewa hauhawar farashin ta zarta kaso 40 cikin 100 a ‘yan watannin baya, abinda ya sanya farashin kayan masarufi yafi karfin miliyoyin ‘yan Najeriya.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada tabbacin cewa ana kokarin shawo kan matsalar karancin abinci kuma nan bada jimawa ba farashin kayan masarufi zai sauko.

Alkaluman baya-bayan nan daga ofishin kididdiga na kasa sun nuna cewa hauhawar farashin ta zarta kaso 40 cikin 100 a ‘yan watannin baya, abinda ya sanya farashin kayan masarufi yafi karfin miliyoyin ‘yan Najeriya.

Sai dai karamin Ministan Aikin Gona Aliyu Abdullahi yace dimbin tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta bijiro dasu, zasu sassauta farashin kayan masarufin.

Ya bayyana a cikin shirin hantsi na tashar talabijin ta Channels na yau Litinin cewar, “za’a ga dimbin tsare-tsaren da aka bijiro dasu domin sassauta yanayin.”

A cewar Abdullahi, “harkar noma abu ne da ya ke da lokaci. A halin yanzu, ana ta aikin gona. A cikin damina muke kuma idan ka kalli gonaki, za ka ga ana ta aikin noma. Shuke-shuken basu zamo abinci ba.”

“Zasu zamo abinci ne kawai bayan kimanin watanni 3. Don haka, kafin wannan lokaci, haka labarin da ka ke nema zai cigaba da kasancewa.”

Ministan yace a baya kasar nan ta dogara ne akan noman damina.

Saidai ya sanar da cewa ma’aikatarsa na kokarin shawo kan matsalar, inda yace “mun gano cewar tsawon shekaru bama daukar noman rani da mahimmanci.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG