Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Janye Harajin Shigo Da Kayan Abinci


Kayan abinci a kasuwar Najeriya
Kayan abinci a kasuwar Najeriya

Ministan Albarkatun Noma da Wadatar Abinci, Abubakar Kyari, wanda ya sanarda hakan a shafinsa na X a yau Laraba, yace za’a aiwatar da matakan da aka bijiro ne cikin kwanaki 180 masu zuwa.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanarda daukar matakai da dama ciki harda bada wa’adin kwanaki 150 domin daina cazar haraji akan kayan abincin da aka shigo dasu cikin kasar a wani sabon yunkuri na dakile hauhawar farashin kayan abincin.

Ministan Albarkatun Noma da Wadatar Abinci, Abubakar Kyari, wanda ya sanarda hakan a shafinsa na X a yau Laraba, yace za’a aiwatar da matakan da aka bijiro ne cikin kwanaki 180 masu zuwa.

A cewar Ministan, hakan zai hada da dakatar da dukkanin cazar nau’ukan harajin akan shigo da wasu nau’ukan kayan abinci ta kan iyakokin Najeriya na tsandauri da teku.

Kayayyakin abincin sun hada da masara da casassar shinkafa mai ruwan kasa da alkama da kuma wake.

Da yake bayyana cewar za’a sanyawa kayan abinci farashin da za’a yi shawara akai, Ministan ya kara da cewa, “muna sani da irin damuwar da ake da ita akan ingancin kayan abincin da za’a shigo dasu, musamman batun jirkita halittarsu. Gwmanati na bada tabbacin cewar za’a kiyaye dukkanin ka’idoji domin tabbatar da kiyaye lafiya da ingancin kayan abincin da jama’a zasu ci.”

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya zata shigo da tan dubu 250 na alkama da masara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG