Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya Na Fuskantar Barazanar Fadawa Kangin Yunwa – Majalisar Dinkin Duniya


Chad Sudan
Chad Sudan

Hukumar ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana fafutukar tara isassun kudade don magance matsalar karancin abinci a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Jami’ai sun ce karuwar tashe tashen hankula a duniya sun sa kasashen da ke neman taimako gwagwarmayar nema wa kansu mafita.

Koke-koken yara masu fama da larurar tamowa sun cika wani asibiti da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda suke jira a yi musu jinyar ceton rai. Asibitin da ke garin Dikwa na da tazarar kilomita 90 daga tsakiyar babban birnin jihar.

An yi jinyar yara fiye da 300 a asibitin a wannan shekarar, kuma sabbin marasa lafiya na zuwa a duk rana. Mai’aktan jinkai sun ce basu da isasshen wurin kula da dukkan marasa lafiyar.

Aliyu Muhammad Sani, shi ne jami'in kula da fannin masu larurar tamowa a asibitin, ya ce akwai majinyata sama da 45 da ke jira a kwantar da su asibitin, "abin da mu ke yi shi ne idan muka je zagayen duba marasa lafiya muka ga cewa akwai wadanda suka murmure, da wadanda suka warke, to sai mu sallamesu, a cewarsa.

Amma ga duk yaro daya da aka sallama, jami'ai sun ce akwai kusan wasu 10 da ke jiran gurbinsa a asibitin. Kuma tsananin yanayin ciwo ne zai sa a tantace wanda ya cancanci a kwantar da shi.

Zainab Musa, wacce rikici ya raba da matsugunninta shekaru 10 da suka wuce, tana zama a Dikwa. Ta ce ana jinyar daya daga cikin tagwayen ‘yayanta.

"Dana ya kamu da rashin lafiya saboda yunwa, bana iya cin abinci yadda ya kamata don in shayar da su duka biyun. Amma a nan yanayinmu ya inganta, suna ciyar da ni sau uku a rana."

larurar tamowa a Afrika
larurar tamowa a Afrika

Yayin da ake da kiyasin yara miliyan biyu da ke fama da larurar tamowa mai tsanani, asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya na UNICEF ya ce Najeriya ce kasa ta biyu a duniya da ta fi yawan yara da suka tsumbure.

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kowace sa’a, yara 100 ‘yan kasa da shekaru biyar a Najeriya ke mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki kuma kashi 20 cikin 100 na yara da ke fama da larurar ne kadai ke samun jinya.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa idan ba a dauki mataki ba, za a ga mummunan sakamako na karancin abinci a wurare irin wannan.

Jami’ai sun ce matsalar karancin abinci da matsalar rashin abinci mai gina jiki, su ne illolin tashe tashen hankulan ‘yan bindiga da aka dade ana yi a yankin, da sauyin yanayi da kuma manufofin gwamnati da suka sanya farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi.

Kayan Marmari Abinci
Kayan Marmari Abinci

Hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya ya haura kashi 40 cikin 100, a cewar ofishin kididdiga na kasar.

A watan Mayu, Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin Najeriya suka kaddamar da shirin neman gudummuwar dala miliyan 306 don magance matsalar karancin abinci ga mutane kimanin miliyan 5 a jihohin da rikicin ya fi shafa.

Amma jami'ai sun ce gudummawar da ake badawa na raguwa.

“Idan aka yi la’akari da yanayin tallafin da Najeriya ke samu a cikin shekaru 10 da suka gabata, za a ga raguwar kudaden da ake samu sosai, saboda batun ba da fifiko ya shigo. Yawan rikice-rikice na karuwa kusan a duk rana, ko wata-wata, ko shekara-shekara," kamar yadda Mohamed Malik kwadinetan Majalisar Dikin Duniya a yankin ya bayyana.

Amma a Dikwa, kungiyoyin agaji na taimaka wa dubban mutane su yi noman abinci a gida ta amfani da hanyoyin da suka dace da yanayin.

“Wadanda ke bin tsarin sun sami amfanin gona da yawa daga filayen da suka noma, sun nema wa kansu hanyoyin samun saukin rayuwa, ta yadda za su tabbatar da samun abinci," a cewar Khalifa Muhammad, na kungiyar Mercy Corps Agricultural and Livestock.

Noman rani (IFAD).
Noman rani (IFAD).

A ranar Litinin 8 ga watan Yuli, Najeriya ta sanar da shirin cire haraji kan wasu kayayyakin abinci da suka hada da alkama da masara domin samun farashi mai sauki.

Amma in dai ba a dauki wani kwakkwaran mataki ba, jami'ai sun ce makomar miliyoyin mutane, musamman yara na tattare da rashin tabbas.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG