Hukumar da ke kididdiga ta NBS a Najeriya, ta ce farashin kayayyaki a kasar ya kara hauwawa a kididdigar da ta yi a watan Yunin 2024.
A cewar hukumar ta NBS, farashin na kayakkin ya karu zuwa kashi 34.19.
Hakan a cewar NBS na nuni da cewa an samu karin kashi 0.24 idan aka kwatanta da wanda aka gani a watan Mayu wanda ya nuna kashi 33.45.
“Hakan na nufin a watan Yunin 2024, karin da aka gani a farashin na kayayyaki ya haura farashin da aka gani a watan Mayun 2024.” In ji hukumar kamar yadda rahotanni suka ruwaito.
Hukumar ta ce tashin farashin kayayyakin da aka gani na da nasaba da karuwar farashin kayan abinci kamar na man gyada, manja, kifi, rogo, dankali, doya da sauransu.
Fitar da wannan kididdiga na zuwa ne yayin da wasu ‘yan kasar musamman a arewaci suke yekuwar a fita zanga-zanga a farkon watan Agusta don bayyan irin halin kuncin rayuwa da jama’a suka shiga.
Wannan kira ya haifar da rarrabuwar kawuna, inda yayin da wasu ke cewa a fita a yi zanga-zangar wasu kuwa cewa suke zanga-zangar ba ita ce mafita ba.
Hukumomin Najeriya na ikirarin suna iya bakin kokarinsu wajen daukan matakan da za su saukaka rayuwar jama’a.
Tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafin man fetur a bara, jama’a suka fara fuskantar matsalolin rayuwa musamman na hauhawar farashin kayayyaki.
Gwamnati ta ce ta dauki matakin ne don rage yawan kudaden da take kashewa.
A watan Mayu, Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Olayemi Cardoso ya ce kayayyakin abincin da gwamnati take saya don rabawa mabukata na daga cikin dalilan da suke kara hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Masana a fannin tattalin arziki da dama sun yi nuni da cewa dole sai Najeriya ta rage dogaro da shigo da kayayyaki idan ana so farashi ya daidaita - matsayar da Shugaban bankin raya kasashen Afirka AFDB, Dr. Akinwumi Adesina ya jaddada a karshen makon da ya gabata.
Dandalin Mu Tattauna