Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’ummar Sudan Na Fama Da Yunwar Da Ba a Taba Ganin Irinta Ba


Yara a Sudan suna cin abinci.
Yara a Sudan suna cin abinci.

Wani sabon rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya ya ce yunwa a Sudan da yaki ya daidaita na cikin wani yanayi da ba a taba ganin irinsa ba, inda sama da mutane miliyan 25 ke fama da matsalar yunwa, wasu kuma 755,000 na cikin mawuyacin hali, da kuma hadarin fadawa yunwa a yankuna da dama.

“Tawagar hukumar samar da abinci ta MDD a Sudan tana aiki dare da rana cikin mawuyacin hali don isar da agajin ceton rai, amma duk da haka wadannan alkaluma sun tabbatar da cewa lokaci ya kure na dakile yunwa,” in ji Cindy McCain, babban darektan hukumar samar da abinci ta duniya a cikin wata sanarwa ranar Alhamis. Ya kara da cewa “Ga kowane mutum daya da muka taimakawa wannan shekara, wasu takwas na bukatar taimako.”

McCain ya ce masu aikin jin kai na bukatar karin kudade cikin gaggawa, don a fadada damarsu sosai ta yadda za su iya bunkasa ayyukan agaji.

Kwararru kan harkokin tsaron abinci sun tattara bayanan ne tsakanin 21 ga Afrilu zuwa 13 ga watan Yuni.

Rahoton nasu na baya-bayan nan na Integrated Food Security Phase Classification, ko IPC, ya ce Sudan na fuskantar matsalar karancin abinci da hukumar ta IPC ta taba samu a kasar. An kafa IPC a cikin 2004.

Masanan sun kammala cewa sama da rabin jama'ar - mutane miliyan 25.6 - ana hasashen za su fuskanci matsalar yunwa ko kuma muni a lokacin bazara, wanda ke gudana daga yanzu zuwa Satumba.

A cikin jihohi 10 cikin 18 na Sudan, mutane 755,000 suna fuskantar IPC 5 - ko matakan bala'i. Wannan ya hada da dukkanin jihohi biyar da suka hada da Greater Darfur da Kudu da Arewa Kordofan da Blue Nile da Al Jazirah da kuma Khartoum.

Kwararru a fannin abinci sun yi gargadin cewa idan rikicin ya ci gaba da ruruwa, akwai yuwuwar kamuwa

da yunwa a yankuna 14 da suka hada da Greater Darfur da Greater Kordofan da jahohin Al Jazirah da kuma wasu wurare masu zafi a babban birnin kasar Khartoum.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG