Bayan fashewar madatsar ruwan da aka samu a watan Satumbar da ya gabata, da ambaliyar da ta mamaye babban birnin jihar, Maiduguri da gonakin da ke kewayensa, al’umma da dama sun fada cikin garari.
Yanzu sun koma karbar tallafi a sansanonin da aka tsugunar da mutanen da yaki tsakanin mayakan Boko Haram masu tsaurin akida da dakarun soja ya daidaita.
Idan haka bata samu ba, suna neman kwadago a gonakin dake kusa inda suke shiga hatsarin fuskantar kisa ko fyade daga ‘yan bindigar dake yankin.
“Yanzu bana iya kuka. Na gaji,” a cewar Indo Usman, wacce ke kokarin fara sabuwar rayuwa a babban birnin jihar, Maiduguri, inda take kiwon dabbobi domin sayarwa a lokacin bukukuwan Sallar Idi, bayan ta sha fama da guje-guje daga hare-haren ‘yan tawaye a kauyukan Borno.
Ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da dukkanin abin da ta mallaka, inda ta tilasta mata da mijinta da ‘ya’yansu 6 komawa rayuwa a daki daya a garin Gubio, a wani rukunin gidajen da ba’a kammala ba dake da tazarar kilomita 96 arewa maso yammacin birnin Maiduguri.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna