Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Lafiyar Najeriya Suna Yunkurin Shawo Kan Cutar Kwalara A Jihar Barno


FILE - Homes and other buildings are partially submerged following a dam collapse, in Maiduguri, Nigeria, Sept 10, 2024.
FILE - Homes and other buildings are partially submerged following a dam collapse, in Maiduguri, Nigeria, Sept 10, 2024.

Jami'an lafiyar Najeriya a jihar Barno dake yankin arewa maso gabashin Najeriya sun ce suna kara kaimi don ganin sun shawo kan annobar kwalarar da ta barke a jihar, biyo bayan ambaliyar ruwan da aka samu a jihar, wanda ya raba sama da mutane miliyan biyu (2,000,000) da muhallan su.

Jihar Borno wace ta kasance babbar cibiyar tashe-tashen hankulan tsattsauran ra'ayin Islama na tsawon shekaru 15 wanda da ya raba dubban mutane da muhallan su wanda ya tursasa musu komawa rayuwa a sansanonin 'yan gudun hijira suna kuma fama da karancin kayayyakin tsaftace jiki da tsaftatacen ruwan sha.

Sai dai, sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a babban binin jihar Maiduguri a 'yan kwanakin baya, ana kyautata zaton akwai karuwar kamuwa da cutar ta kwalara, bisa bayanan kwamishanan lafiya na Jihar.

Baba Mallam Gana yace, "Muna samun karuwar alkaluman mutanen da suke fama da guda wa, lamarin da ake kyautata zaton cewa kwalara ce, wanda baya rasa nasaba da iftila'in ambaliyar ruwan."

Kwanishanan ya ce ya zuwa yanzu, babu mutum guda da ya mutu, sannan gwamnati tana daukar matakan shawo kan lamarin.

"Domin rage tasirin barkewar cutar ta kwalara, ma'aikatar lafiya ta jihar Barno ta samo maganin rigakafin cutar kwalara da ake sha guda dubu 300,000 daga ma'aikatar lafiya na tarayyar Najeriya, ya ce "muna matukar godiya da wannan taimakon, sannan mun rarraba maganin rigakafin a sansanonin 'yan gudun hijira da al'ummomin da ambaliyar ta shafa."

Akalla mutane 500 ne aka ba da rahoton suna gudawa, a cewar Gana, inda lamarin ya fi kamari a kananan hukumomi 5.

Daga cikın matakan da gwamanti ta dauka don shawo kan matsalar, an mai da cibiyar lafiyar al'umma ta gaggawa ta jihar zuwa cibiyar gudanar da ayyukan sa ido, ba da sanarwa a game da hadari da tuntubar al'umma, da kuma gudanar da muhimman ayyukan lafiya, kariya daga kamuwa da cutar, tsaftace ruwa da kula da tsafta.

Muhammad Bashir- Abdullahi, shine jami'in dake kula da al'amuran lafiya a Maiduguri. Muhammad Bashir ya ce, Mutane da dama sun kamu da cutar cikin 'yan makonnin da suka gabata zuwa 'yan kwanakin nan, sannan ya ce "mun yi nasarar basu kulawar da ta dace, lamarin ya shafi al'ummomi da dama a Maiduguri, musamman ma mutanen da ke sansanin Gubio. Mutane da dama sun kamu da cutar a can.

Kungiyar likitoci ta Medicines San Fromtiers ta kafa cibiyar kula da masu kwalara da za a iya fadada ta ta dau gadaje 100 in akwai bukatar hakan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG