Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Fidda Sabon Gargadi Kan Yiwuwar Ambaliya A Kasar


This aerial view shows houses submerged under water in Maiduguri on September 10, 2024.
This aerial view shows houses submerged under water in Maiduguri on September 10, 2024.

Sanarwar da babban daraktan hukumar kula da koguna ta Najeriya (NIHSA), Umar Ibrahim Muhammad, ya fitar tace madatsar ruwa ta Jebba na sakin rarar ruwa kamar yadda hukumar dake kula da madatsar ruwan Kainji ta tsara, inda zuwa yanzu ta ba da tazarar sentimita 53.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fidda sabon gargdi game da yiyuwar samun ambaliyar ruwa a kasar.

Sanarwar da babban daraktan hukumar kula da koguna ta Najeriya (NIHSA), Umar Ibrahim Muhammad, ya fitar tace madatsar ruwa ta Jebba na sakin rarar ruwa kamar yadda hukumar dake kula da madatsar ruwan Kainji ta tsara, inda zuwa yanzu ta ba da tazarar sentimita 53 domin ba da damar nazarin sauyi a gudanawar ruwan.

Da yake yin karin haske game da alakarsu da hukumomin kula da madatsun ruwa na cikin kasa dana ketare, Umar Ibrahim Muhammad, yace nihsa ta dukufa wajen magance matsalar ambaliyar koguna domin bunkasa tattalin arziki da rayuwar ‘yan Najeriya.

Ya kuma kara da cewar yawan ruwan dake kogin neja ya fara raguwa tun farkon watan Oktoban da muke ciki.

Har ila yau ya bukaci ‘yan Najeriya dasu kiyaye ka’idojin tunkarar ambaliya, inda ya jaddada aniyar ma’aikatarsa ta magance matsalar ambaliya a Najeriya.

Gargadin na zuwa ne sakamakon rahotannin baya-bayan nan game da munanan ambaliyar ruwan da aka gani a tarihin najeriya, inda ta birnin Maiduguri, fadar gwamnatin jihar Borno ke sahun gaba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG