Shugaban yana bayani ne a washe garin zaman da majilisar dokoki ta gudanar domin kwaskware dokokin zabe.
To amma da take bayyana matsayin akan wadannan sauye-sauye?
Kotun tsarin mulki kasa tace an sabawa kundin mulkin kasa.
Wannan yasa Salisu Amadu wani dan rajin kare demokaradiyya ya jinjina wa kotun.
‘’Ita kotun ALLAH yayi mata albarka kuma taci gaba da watsar da abubuwan da basu halarta ba, abinda ya shafi kundin zabe da kundin kasa, da dokoki na kasa ba anayin su bane domin sabo da mutum guda, a’a anayin ne sabo da kasa gaba daya domin al’umma ta samu sala’’.
Ga Sule Mummuni Barma da Karin bayani 2’29
Facebook Forum