Fashewar wani bam a garin Waza dake jihar Arewa mai nisa a jamhuriyar Kamaru yayi sanadiyyar rayukan mutane 14 wasu 32 kuma suka jikkata.
An garzaya da mutanen da suka raunata zuwa Asibitin garin Marwa don basu kulawa ta musamman.
A cewar Mallam Bukar mutumin da ya tsira da kyar a harin, ya ce mutane dayawa na kwace a kasa wasu sun mutu wasu kuma sun raunata.
Har ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin harin. Sai dai kungiyar Boko Haram ta dade tana kai ire-iren wannan hari a yankunan tafkin Chadi da ya hada da Kamaru da Nijar da Najeriya.
A cewar ‘daya daga cikin masu baiwa shugaban kasar Kamaru shawara, Mista Lauren, harin da aka kai garin Waza ya basu mamaki, kuma zasu duba hanyar da zasu toshe duk hanyoyin da maharani Boko Haram ke bi wajen kaddamar da harin ta’addanci.
Sanadiyyar hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa Kamaru, sama da mutane 2,300 suka rasa rayukansu, haka kuma yayi sanadiyyar kwararar ‘yan gudun hijirar Najeriya kimanin dubu 50 a jihar Arewa mai Nisa.
Domin karin bayani saurari rahotan Garba Awal.
Facebook Forum