Jami'in gwamnatin Najeriya da ke fitar da bayanai kan ayyukan ta'addanci, Mr. Mike Omeri, ya ce makasudin hadin gwiwar dakarun makwabtan kasashen Najeriya da ke fafatawa da ‘yan Boko Haram yanzu haka shine a ga cewa an murkushe ‘yan kungiyar, da kuma samar da tsaro da zaman lafiya a kasar da makwabtan ta.
Wannan bayanin na kakakin gwamnatin Nigeria ya biyo bayan wasu kalamai da shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya yi, cewa ya san inda madugun kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya ke, kuma ya ba shi zabin ya ajiye makamansa ko a kashe shi.
Mr. Mike Omeri ya ce kama Abubakar Shekau, wanda ya yi sanadiyar hallaka dubban jama’a, muhimman abu ne a yunkurin da a ke yi na murkushe ‘yan tawayen.
Ya kuma kara da cewa babu wani aibi ko da ba sojojin Najeriya ne su ka kama Shekau ba, ko ma su wa suka kama shugaban kungiyar zai zama abin farin ciki don ba gasa a ke yi ba, kuma ba ‘yan Najeriya kadai ‘yan kungiyar ke hallakawa ba.