Shugaban kasar Chadi, Idris Derby yace sojojinsa sun san inda Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram yake, a saboda haka yayi kira ga shi Shekau da yayi saranda ko kuma a kashe shi.
Laraba shugaban na Chadi yayi wannan furuci a birnin Ndjamena, wajen wani taron yan jarida na hadin gwiwa da shugaban jamhuriyar Niger Mahamadou Issoufou wanda ya kai ziyara kasar Chadi. Dukkan shugabanin biyu sun lashi takobin cewa idan Allah ya yarda za'a murkushe yan kungiyar Boko Haram.
Haka kuma Mr Derby yace, Shekau ya tsalaka rijiya da baya a lokacinda sojojin Chadi suka yantar da garin Dikwa jihar Borno arewa maso gashin Nigeria a ranar Talata. Mr Derby yace in dai Abubakar Shekau bai yi saranda ba, to abinda ya samu yan tawayen da aka kashe a Dikwa, shima haka zata same shi.
Kasashen Chadi da Niger da kuma Kamaru, a watan Janairu suka tura sojoji domin taimakawa Nigeria a yakin da take yi da yan kungiyar Boko Haram, kuma har sun samu nasarar kwato birane da dama da yan Boko Haram suka mamaye a jihohin Borno da Yobe.