Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram: Kaikayi Ya Koma Kan Mashekiya a Diffa


Kunar bakin wake
Kunar bakin wake

Asara ta koma kan Boko Haram yayinda tayi yunkurin kai hari na biyu a Diffa

Wata ‘yar kunar bakin wake ta tarwatsa kanta a garin Diffa na Jamhuriyar Nijar, kwana daya bayanda hukumomi suka ayyana dokar ta baci sabili da hare haren mayakan kungiyar Boko Haram na Najeriya.

Gwamnan jihar Diffa Yakoubou Soumanou Gawo ya shaidawa Muryar Amurka cewa, ‘yar kunar bakin waken ta yi yunkurin kaiwa sojojoji hari jiya Laraba amma aniyarta ta bita, ta karasa da kashe kanta kadai.

An rufe makarantu da cibiyoyin kasuwanci a Diffa yayinda jama’a suka zauna a gida ko kuma suka nemi kauracewa garin dake kan iyaka da Najeriya. Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hari a Diffa ranar Jumma’a da kuma Litinin amma dakarun kasar Nijar da kuma Chadi sun fatattake su.

Tun farko, dakarun kasar Chadi sun ce sojojinsu sun dakile wani yunkurin kai hari da mayakan Boko Haram suka yi a garin Gamboru kan iyaka da Kamaru. Bisa ga kamfanin dillancin labarai na Reuters, rundunar sojin tace ta kashe mayaka goma sha uku a bata kashin da suka yi.

Kasar Chadi ta tura dakaru Gamboru makon da ya gabata a cikin shirin yaki da kungiyar Boko Haram da ake yi a shiyar. Kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru da Nijar da kuma Benin sun yi alkawarin tura dakaru dubu takwas da dari bakwai a wani yunkuri na musamman na yaki da mayakan.

Dakarun Najeriya sun fara yakar kungiyar Boko Haram tunda ta fara tada kayar baya a shekara ta dubu biyu da tara.

XS
SM
MD
LG