Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Iyaye Ke Cewa Game Da Kyauta Tsakanin Samari Da 'Yan Mata?


Iyaye sun tofa albarkacin bakin su a game da tasirin kyauta tsakanin samari da 'yan mata koda shike sun danganta abin da yadda ake gudanar da harkokin aure a shekarun da suka gabata.

A shekarun baya, yawancin lokuta ana daurawa 'yan mata aure ba tare da sun san ko wanene saurayin ba, kuma haka zata hakura ta zauna da mijin ta cikin kwanciyar hankali.

Samari kan bada kyauta ga 'yan matan su ta hanayar aikawa da sakon zuwa ga iyayen budurwar ne, sai su kuma iyayen su dauki wannan kyauta su mikawa yariyar. A yanzu yanayin ya canza, wata yarinyar ma baza ta bari iyayen ta su san ta amsa ba har sai wani abu ya gitta tsakanin su wanda zai sa asirin su ya tonu.

A cewar iyayen, idan yarinya ko budurwa ta sa ranta a karbar kyaututtuka daga samari, zai yi wuya ta gane wanda ke kaunar ta da gaskiya domin so na gaskiya baya la'akari da kudi, yakan ta'allaka ne akan soyayya kawai.

Domin tafka muhawara, ku biyo mu ta shafin mu na; Dandalinvoafacebook.com

Ga cikakken shirin.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG