Matasa da yawa yanzu sun fara rungumar sana'o'i don kyautatawa rayuwarsu ba sai sun yi dogaro ga gwamnati ko wani ba don biyan bukatunsu na yau da kullum.
Wani matashi dan makaranta, mai suna Tijjani Jibrin Garba ya fadi cewa kasancewarsa dan makaranta bai hana shi yin sana'a ba don yanzu haka ya iya gyaran wuta da wasu na'urorin, yana kuma tukin manyan motoci da kanana.
Tijjani ya ce, saboda makarantar da ya ke zuwa, ba ko da yaushe ya ke samun sararin yin wasu abubuwan ba amma sana'ar da ya fi samun kudi ita ce ta kwangilar jigilar jama'a zu zuwa wasu wurare, amma akwai masu agaza mashi a fannin makaranta.
Ya kara da yin kira ga gwamnati akan ta bude hanyoyin samawa matasa aiki ko sana'o'i in sun gama makaranta. Don yanzu haka akwai wadanda sun kammala karatunsu amma samun aiki ya gagara. Ya kuma ce, ya kamata gwamnati ta dinga wayar wa matasa da kai akan yadda zasu zama abinda suke sha'awa nan gaba.
Ga hirar Tijjani Jibrin Garba da Zainab Babaji.