Rahotanni daga jahar Bauchi a Najeriya sun bayyayan yadda wani matashi mai suna Nasiru Audu mai shekaru 25 yayi batan dabo a shekarar 2009, sa'an nan daga baya aka gano gawar sa a cikin wata rijiya.
Kamar yadda mujallar daily post ta wallafa, kakakin jami'an tsaron 'yan sandan jahar Haruna Mohammed ya bayyana cewar an riga an damke wadanda suka aikata wannan aika aika.
Matashin dan asalin kauyen Judo ne dake karkashin karamar hukumar Ningi, kuma sun yi wata 'yar gardama ce tsakanin sa da wani matashi a kauyen su mai suna Bature Abdul dan shekaru 35, wanda ya hada baki da yayansa mai suna Babangida Abdul suka jefa gawar cikin rijiya a lokacin da suka lura cewar bashi da rai.
Kakakin ya kara da cewar sun rarraba mutanen su a kauyen ne har saida suka gano bayyanar afkuwar lamarin, wanda daga baya suka fada wa mai unguwar kauyen mai suna Mohammed Bello, shi kuma ya ce kada su fadawa kowa.
Mai magana da yawun jami'an tsaron ya bayyana cewa a yanzu haka cafke duka wadanda suke zargi da hannu a cikin lamarin, kuma suna ci gaba da bincike kafin daga baya zasu mika su ga kotu domin yanke masu hukunci.