Kasancewar akwai ruwa mai kwaranya zai iya saukaka rayuwar ‘yan sama jannati wadanda ke kai ziyara, ko suke zaune a duniyar Mars. Za’a iya amfani da ruwan wajen sha da samar da iskar oxygen, da man kumbo. Hukumar NASA na da kudurin aika mutane can cikin shekarun 2030.
Hujjar ruwa mai kwranya ta kunshi siraran magudanan ruwa masu duhu a bangon wadanda ke bayyana su kara girma a wannin da suka fi zafi na duniyar Mars, su kuma bace a sauran shekara.
Duniyar Mars na da sanyi kwarai ko da lokacin zafi ne, na samun magudan ruwan ne a wuraren da yanayin shi ya haura -10, a ma’aunin Fahrenheit. Amma gishiri zai iya rage karfin daskarewar ruwa ya narkar da kankara.
Ba a san daga inda rowan yake ba samuwa ba. Masana kimiyya sun yi nuni da cewa zai iya zama kankara dake narkewa, ko wata mabulbular ruwa a karkashin kasa, ko tururin ruwa daga sararin dunirat Mars, ko wasu abubuwa daban.