Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Damu Da Tasirin Ambaliyar Ruwa A Najeriya


Barnar Da Ambaliyar Ruwa Yayi A Jihohin Adamawa Da Taraba
Barnar Da Ambaliyar Ruwa Yayi A Jihohin Adamawa Da Taraba

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa dangane da ambaliyar ruwa a Najeriya da ya shafi rayukan maza da mata da kuma yara sama da miliyan 2.8.

Mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a shedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York na kasar Amurka.

A cewar hukumomin Najeriya, sama da mutane 600 ne suka mutu, yayin da mutane miliyan 1.3 suka rasa matsugunansu.

“Mun damu matuka cewa ambaliyar ruwan za ta kara dagula matsalar karancin abinci da ta yi kamari, da matsalar rashin abinci mai gina jiki a Najeriya. Fiye da kadada 440,000 na gonaki sun lalace a wani bangare ko kuma gaba daya, a daidai lokacin da mutane sama da miliyan 19 a fadin Najeriya ke fuskantar matsanancin karanci abinci.”

Barnar Da Ambaliyar Ruwa Yayi A Jihar Adamawa
Barnar Da Ambaliyar Ruwa Yayi A Jihar Adamawa

Mai magana da yawun Majalisar ya ce mai yuwuwa noman hatsi zai ragu da kashi 3.4 cikin 100, idan aka kwatanta da shekarar 2021, saboda ambaliyar ruwa da tsadar kayan noma da rashin tsaro, a cewar hukumar FAO.

“Tun daga watan Yuli da ya gabata, hukumomin tarayyar Najeriya sun samar da abinci, abubuwan da ba na abinci ba, da kuma tsaftataccen ruwan sha ga dubban gidaje da abin ya shafa.”

Ya kara da cewa “Mu da abokan aikinmu na jinkai muna tallafawa gwamnati, da tantancewa da taimakawa, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, da kuma sauran sassan Najeriya da abin ya shafa.”

“Mun samar da matsugunai na gaggawa, kuma muna aiki don samar da magudanun ruwa na yanki, jakunkunan yashi, da kuma kewaye matsugunai don rage tasirin ambaliyar ruwa”, in ji shi.

NAN

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG