Malam Sani Garba Mai Kifi, shugaban kungiyar ‘yan Achaba a wannan jiha.
Cewa yayi “A halin yanzu muna gidajenmu, dama kuma shi a kullum talaka haka yake, idan an sa doka ya kamata a bi doka.
Yace bai san abubuwan da suke faruwa ba a halin yanzu, amma sun samu nutsuwa daga abubuwan da suka gani a baya.
Ya kara da cewa ya kira sauran ‘yan achaba yace musu su bi doka.
Wani Malam Zakari cewa yayi dokar ta shafi rayuwar mutane saboda daruruwan mutane sun tagayyara.
Yace abu ne wanda ba’a kwana da shi, aka tashi da shi. Galibin mutane sai sun fita kafin su sami abinda zasu ci a kullum, kuma idan aka wayi gari an saka musu doka kar su fita na awa 24 ko sama da haka ma, abu ne wanda ya shafi talakawa da dama.