A wurin wani taro na masu ruwa da tsaki wanda Muryar Amurka ta shirya a Damaturun Jihar Yobe, akasarin masu jawabai sun ce rashin tarbiyya daga gida, da talauci da kuma rashin ayyukan yi, sune suka jefa matasa cikin fitinar da yanzu ta addabi Yobe da sauran arewacin Najeriya.
Wata mai halartar taron ta ce rashin cusa ma yara akidar sanin matsayin iyaye da makwabta da al'umma, na daya daga cikin abubuwan da suka sanya matasanmu su na tashi babu tarbiyya.
Wani malami yace musamman rashin aikin yi, yana sa matasa su rungumi abubuwan da ba su da kyau, tunda ba su da wani zabin.
Yace babban abin yi shi ne tabbatar da bin doka da oda, daga sama har zuwa ga kasa kan talaka. Haka kuma an bayar da shawarar a tattauna da 'yan bindigar dake kawo rashin tsaro a yankin, tare da rokon 'yan Boko Haram da su dubi irin hali na rashin kwanciyar hankalin da suka jefa iyaye da 'yan'uwansu a ciki.
Ga rahoton Sa'adatu Mohammed daga Damaturu.