Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubakar Shekau Ya Musanta Kulla Tsagaita Wuta


Hoton da aka ciro asabar 13 Yuli, 2013 daga wani faifan bidiyo da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, yayi.
Hoton da aka ciro asabar 13 Yuli, 2013 daga wani faifan bidiyo da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, yayi.

Shugaban kungiyar da aka fi sani da sunan Boko Haram yace ba zasu taba tattaunawa da gwamnatin Najeriya ba, amma masu fashin baki su na ganin kamar kungiyar ta rarrabu ne

A bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnati Lidda'awati Wal Jihad, wadda aka fi sani da sunan Boko Haram, ta yarda da shirin tsagaita wuta, shugaban kungiyar, Imam Abubakar Shekau, yayi wani faifan bidiyo inda a ciki yake musanta wannan batu. Sai dai kuma yayin da Shekau yake kiran da a kara kai hare-hare, masu fashin baki da yawa sun ce kawunan kungiyar Boko Haram sun rarrabu sosai, kuma da alamun wani bangare nata ya yarda da tsagaita wutar.

A cikin wannan sabon bidiyon, inda yayi magana da harsunan Hausa, Larabci da Ingilishi, Shekau ya ce sanarwar da gwamnati ta bayar ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, "karya" ce, kuma ba za a samu zaman lafiya ba sai an maye gurabun makarantun Boko da na Islamiyya. Yayi kiran da a kawo karshen mulki irin na dimokuradiyya da amfani da tsarin mulki.

Abubakar Shekau ya yaba da harin da aka kai kan makarantar sakandaren gwamnati a garin Mamudo, dake kusa da Potiskum a Jihar Yobe, inda aka kashe mutane har 42 a lokacin da 'yan bindiga suka bude wuta. Akasarin wadanda aka kashe yara ne, amma kuma Shekau yace ba su ne suka kashe yaran ba.

Masu fashin baki suka ce koda yake Shekau yace ba mutanensa ne suka kashe yaran ba, watakila wasu mutane ne dake kiran kansu wani bangare na kungiyar.

Kungiyar Boko Haram, kungiya ce ta boye, wadda a kullum take sauyawa, in ji tsohon jakadan Amurka a Najeriya, kuma babban jami;i a Majalisar nazarin Hulda da Kasashen Waje ta Amurka, John Campbell.

Yace, "ina jin cewa wannan ya tado da tambayar wai shin wacece kungiyar Boko Haram? A zahirin gaskiya, kungiya ce dake warwatse, dake kunshe da masu ra'ayoyi dabam-dabam, wadda ba ta da wani tsarin shugabanci kwaya daya tak fitacciya."

Campblell yace tana a saboda rarrabuwar kungiyar, tana yiwuwa gwamnatin Najeriya da gaske take yi cewa ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da wani bangaren Boko Haram, amma kuma tana yiwuwa shi ma Abubakar Shekau gaskiya yake fada cewa bai cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin ba.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG