A jihar Adamawa, daya daga cikin jihohi uku dake karkashin dokar ta baci jama'a na kokarin shirin bukin sallar karshen azumi.Wakilinmu Ibrahim Abdulaziz Biu ya zagaya garin Yola babban birnin jihar Adamawa ya ga irin shirin da jama'ar jihar ke yi. Duk da dokar ta bacin ya ga teloli suna harkar dinkin salla kamar yadda suka saba can baya. Teloli da yawa sun samu aikin yi to amma ba duka bane ke darawa a wannan lokacin domin wasu sallar ta samesu a wani hali na rashin kudi. Wani magidanci Malam Garba Usman ya ce rashin biyan albashi na cikin dalilan da suka jawo masa rashin kudi a wannan lokacin. Ya ce dakyar suka iya yin kashi daya cikin kashi uku na abubuwan da suke yi da lokacin wadata. 'Yan kasuwa ma na kokawa. Wani mai sayar da tufafi ya ce sun sayo kaya amma babu masu saye domin rashin kudi.
Garin Yola ya soma cika da mutane har ma an soma karbar harami da bakin mahawa dawakai a fadar Lamidon Adamawa bikin salla kamar yadda aka saba yi.
Ibrahim Abdulazi Biu nada karin bayani.