Gwamnatin jihar Filato ta sanya dokar hana fita ne na sa'o'i 24 a karamar hukumar Jos ta Arewa da garin Bukur a karamar hukumar Jos ta Kudu.
A wata sanarwa daga ofishin gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, dokar hana fitar mataki ne na dakile ayyukan wasu bata gari da ke son yin amfani da zanga-zangar lumana da ake yi na jan hankalin gwamnati ta samar wa al'umma mafita kan matsalolin rayuwa, don su lalata ko sace dukiyar jama'a.
Sanarwar ta ce bayan yin nazarin tsaro da gwamnati tayi da jami'an tsaro ta gano cewa matasan dauke da adduna, wukake, sanduna da sauran muggan makamai, sun dauki aniyar jirkita zaman lafiya da jihar ke da shi tun lokacin da aka fara zanga-zangar.
Jakadan zaman lafiya, Usman Big Seven, ya ce yadda ya ga batagarin sun fara farfasa dukiyar mutane ne ya sa, matakin da gwamnatin ta sanya na hana fita ya dace.
Ita ma Rachael Musa ta ce matasan da ta gani dauke da makamai sun ba ta tsoro.
Mai fashin baki kan lamura, Mr. Japhet Philip ya ce tutocin kasar Rasha da matasan ke dauka, kira ne kan kasar ta kawo musu dauki.
Kokarin jin karin bayani kan dokar hana zirga-zirgar daga komishinan yada labarai da sadarwa na jahar Filato, Musa Ibrahim Ashoms yaci tura, duk da sakon kar ta kwana da na aike masa, bai maido min da martani ba.
A jawabinsa ga 'yan Najeriya, shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci masu zanga-zangar su janye, don ba da zarafin tattaunawa don samun mafita.
Tun a ranar daya ga watan Agusta ne dai 'yan Najeriya a jihohi da dama na kasar suka shiga zanga-zangar neman sassauci a tsare-tsaren gwamnati da suka haifar da matsalolin rayuwa.
A jihar Kaduna da ke makwabtaka da jihar ta Filato, gwamnatin jihar ta saka dokar hana fita a biranen Kaduna da Zaria.
“Ga dukkan alamu wasu bata-gari sun karbe ragamar wannan zanga-zangar inda suke fasa shagunan mutanen suna bata kayayyakin gwamnati da na jama’a.” In ji sanarwar da Ministan cikin gida da samar da tsaro Samuel Aruwan ya fitar.
“Ana ba jama’a shawara su zauna a gida yayin da jami’an tsaro suke ci gab da kare lafiyar jama’a.
A baya, jihohin Kano, Katsina, Yobe, Borno da Nasarawa duk sun dauki wannan mataki yayin da ake ci gaba da zanga-zangar.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Dandalin Mu Tattauna