Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga Zanga Ta Rikide Zuwa Tashin Hankali A Wasu Sassan Burtaniya Bayan Kisan Wasu Yara 3


ISRAEL-PALESTINIANS/PROTESTS-BRITAIN
ISRAEL-PALESTINIANS/PROTESTS-BRITAIN

Masu zanga-zanga sun kai hari kan 'yan sanda tare da tada wuta a birnin Sunderland da ke arewa maso gabashin Burtaniyya a ranar Juma'a yayin da tashin hankalin ya bazu zuwa wani garin a arewacin kasar, biyo bayan kisan wasu yara uku a ranar Litinin a Southport.

Masu zanga-zangar nuna kyamar baki sun jefi ‘yan sanda da duwatsu a kusa da wani masallaci a birnin, kafin daga baya suka jirkitar da motoci, suka cinna wa wata mota wuta sannan suka tayar da wuta a kusa da wani ofishin ‘yan sanda, kamar yadda kafar yada labaran BBC ta bayyana.

“Tsaro da kariyar jama’a su ne babban abin da muka sa a gaba, kuma da muka gano cewa an shirya zanga-zanga, mun tabbatar da cewa an kara yawan jami’an ‘yan sanda a cikin birnin,” a cewar shugabar ‘yan sandan Northumbria, Helena Barron a cikin wata sanarwa.

"Da maraicen Juma’a wadannan jami'an sun gamu da mummunan tashin hankali wanda abin takaici da Allah wadai ne," a cewar Barron.

Shugabar ‘yan sandan ta kara da cewa an kwantar da jami'an 'yan sanda uku a asibiti, kuma an kama mutane takwas bisa laifukan da suka hada da tada zaune tsaye da kuma sata.

Zanga-zangar da aka yi a Sunderland na daya daga cikin wasu fiye da goma sha biyu da ‘yan rajin kyamar baki suka shirya a fadin Birtaniya a karshen mako, ciki har da a kusa da akalla masallatai biyu a birnin Liverpool, birnin da ke kusa da inda aka kashe yaran.

Haka kuma, an shirya yin zanga-zangar adawa da kyamar baki a wurare da dama.

Jami'ai sun ce an baza 'yan sanda a fadin kasar a ranar Juma’a kuma masallatai sun dauki tsauraran matakan tsaro.

Ana tuhumar wani matashi dan shekara 17 da laifin kisan yaran (mata) uku a wani hari da wuka a wani wurin koyar da rawa a garin Southport da ke arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya girgiza al’ummar kasar.

Abubuwan tada hankali sun faru a cikin kwanakin da suka biyo baya a Southport, da garin Hartlepool, da kuma birnin Landan a matsayin martani ga bayanan karya da aka yada a shafukan sada zumunta, wadanda ke ikirarin cewa wanda ake zargi da harin wukar bako ne mai tsattsauran ra’ayin addinin Islama.

A wani yunkuri na kawar da ikirarin, 'yan sanda sun jaddada cewa matashin da ake zargi a Biritaniya aka haife shi.

A ranar ta Juma'a, Firai Minista Keir Starmer ya kai ziyara karo na biyu a Southport tun bayan kisan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG