Shugabar kungiyar Madam Serah Pam, tace abun bakin ciki ne ganin yadda aikata irin wadannan laifuffuka suke kara karuwa a yankin, kamar jama'a sun daina tsoron Allah.
Tace muddin hukumomi suka tsaya da gaske wajen hukunta masu irin wadannan laifuffuka, hakan zai zama darasi ga na baya, idan har suna tunanin aikata fyade.
Ita ma shugabar kungiyar mata musulmi ta FOMWAN reshen jihar Flato Malama Mairo Sani, tace akwai bukatar iyaye mata su kara sa ido kan 'ya'yansu mata, su san irin mutane da suke mu'amala da su.
Shugabar kungiyar mata ta kiristoci Pastor Mary Shikse, tace daya daga cikin matakan da kungiyar take dauka shine fadakarwa ga iyaye mata kan alamomi da suka kamata su lura daga diyansu mata.
Haka ma kungiyar mata lauyoyin ta bayyana irin hadin kai da take yi da sauran kungiyoyi wajen yaki da wannan muguwar dabi'a.
Ga karin bayani.