Yau laraba ake sa ran shugaban Amurka Barack Obama zai bayyana shirin janye sojojin Amurka daga Afghanistan da zai kai dubu goma zuwa karshen wan nan shekara.
Anji Jami’an hukumar tsaro suna cewa da farko shugaba Obama zai bukaci a janye sojoji dubu biyar, san nan daga bisani a sake janye wasu dubu biyar a karshen shekara.
Duk da haka kakakin fadar white House, Jay Carney, jiya talata yayi gargadi ga kafofin yada labarai da su nisanci saci fadi kan batun janye sojojin. Yana cewa shugaban na Amurka zaiyi bayani yadda za’a aiawatar da shirin janyewar,kamar yadda yayi alkawari a jawabi da yayi cikin watan Disemban 2009.
A cikin jawabin a 2009 da shugaban a gabatar a makarantar horasda sojoji dake New York, Mr. Obama yayi alkawarin fara janye sojojin Amurka cikin watan Yulin bana.
Ahalin yanzu kuma, jami’an Afghanistan sun bada labarin mayakan sakan Taliban sun kashe akalla ‘yansanda 12 ko suka jikkata su a wasu hare hare daban daban har biyu da suka kai kan wani wurin duba motoci.