Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran za ta gwada makami mai linzami mai dogon zango


Jiragen ruwa yakin Iran
Jiragen ruwa yakin Iran

Iran ta ce a yau Asabar za ta harba makamai masu linzami masu

Iran ta ce a yau Asabar za ta harba makamai masu linzami masu dogon zango, a matsayin wani bangare na atisayen sojin da ta ke yi a tekun Fasha.

Wannan sanarwar ta jiya Jumma’a ta zo ne adaidai lokacin da jijiyoyin wuya ke ta kara tashi tsakanin Iran da manyan kasashen yammacin Duniya kan barazanar Iran ta katse jigilar man fetur ta mashigar ruwan Hormuz.

Kamfanin Dillancin Labaran da ke dasawa da gwamnatin ta Iran mai suna Fars, ya ruwaito wani babban sojin ruwan Iran admiral Mahmoud Mousavi na cewa, sojojin ruwa za su gwaggwada makamai masu linzami iri-iri, ciki har da masu dogon zango, a cigaba da atisayen sojin da aka fara tun ran 24 ga wannan wata na Disamba. Ya ce harbe-harben gwajin su ne mataki na karshe na atisayen, don a ja damarar sojojin ruwa don tinkarar abokan gaba a kowane yanayi na yaki.

Makaman Iran sun hada da makami mai linzami na Shahab-3, wanda zai iya isa kasar Isira’ila da kuma wasu sansanonin sojin Amurka da ke gabas ta tsakiya.

Fiye da kashi daya bisa uku na mayukan fetur da ake jigilarsu ta jirgin ruwa, ana bi da su ne ta mashigar ruwan Hormuz. Rufe shi zai hana samar da wani bangare na mai na wani lokaci ya kuma kawo tsadar man a fadin duniya.

Hedikwatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta ce ba fa za a lamunta ba, da duk wani yinkuri na kawo cikas ga jigar mai ta mashigar.

Can kuma dabam, kamfanin dillancin labaran Associtaed Press ya ruwaito wani jami’in Ma’aikatar man Saudiyya na cewa idan ta kama, za su kara yawan man da su ke samarwa daga yankin na Fasha don a cike duk wani gibi.

XS
SM
MD
LG