Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amirka tayi Allah wadai da ftsarin da wasu mayakan Amirka suka yi akan gawarwarkin yan Taliban


Hoton vidiyon sojojin da aka sa a shafin Youtube na dandalin yanar gizo daya nuna sojojin suna fitsari akan gawarwarkin
Hoton vidiyon sojojin da aka sa a shafin Youtube na dandalin yanar gizo daya nuna sojojin suna fitsari akan gawarwarkin

Amirka ta la'ani hoton vidiyon wanda da alama ya nuna wasu sojojin kundubalan Amirka suna fitsari akan gawarwarkin mayakan kungiyar Taliban

Amirka tayi Allah wadai da hoton vidiyo, wanda bisa dukkan alamu ya nuna wasu sojojin kundubalam Amirka suna yin fitsari akan gawarwarkin mayan kungiyar Taliban.

Jiya Alhamis sakataren tsaron Amirka Leon Panetta yace hoton vidiyon abin yin tir ne. Ya kuma lashi takobin cewa za'a hukunta wadanda keda alhakin aikata wannan aikin asha.

Leon Panetta ya baiwa rundunar sojojin kundubala da shugaban jami'an tsaron kungiyar kawancen tsaro ta NATO a Afghanistan umarnin sun binciki al'amarin.

Itama sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton tabi sahin sakataren tsaron Amirka wajen yin tir da hoton vidiyon.

Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan yace gwamnatinsa ta damu sosai da wannan hoton vidiyon daya baiyana da zaman cin mutunci ne.

Ma'aikatar tsaron Amirka, wadda ake cewa Pentagon a takaice tace bata da wani dalilin tababan sahihancin hoton vidiyon.

Jiya Alhamis jami'an Amirka suka ce rundunar sojojin kundubala ta gano ko su wanene sojojin da suka aikata wannan akili, to amma ba'a baiyana sunayensu ba.

Shi ma kwamanda rundunar sojoji kundubala Janaral James Amos yace ya bukaci sojojin kundubala da mayakan ruwa su gudanar da nasu binciken akan al'amarin.

Hoton vidiyon dai ya nuna sojojin kundubala sanye da unifam suna yin fitsari akan gawarwarki guda uku.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG