Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan Belgium sun tsinci kwamfuta cike da bayanan ofishin firayim ministan kasar


'Yansandan kwantar da tarzoma na kasar Belgium
'Yansandan kwantar da tarzoma na kasar Belgium

‘Yansandan kasar Belgium sun sami hotuna da taswirar ofishin Firayim Ministan kasar a cikin wata kwamfuta da aka yar a cikin kwandon shara a rukunin gidajen ‘yan ta’addar da ake zargi da harin kasar na makon da ya gabata suka taba zama

Jaridun Belgium da dama sun bada labarin cewa, an tsinci na’urar kwamfutar ta hannu ne a lokacin da ‘yan sanda suka kai samame a unguwar Rue Max Roos da ke Schaerkbeek sa’o’i da dama bayan kai harin na tashar jiragen sama data kasa a Brussels da ya hallaka mutane 32 ya jikkatawasu da dama.

Wani jami’in gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa saboda har yanzu ana binciken lamarin, ya tabbatar da labaran da suka bayyana, ya kuma kara da cewa, har yanzu ba wata alama da ta nuna cewa Firayim Ministan na fuskantar barazanar mahara.

Yace, kwamfutar an sameta cike da bayanai daban daban da aka samu ta hanyar laluben yanar gizo game da ofishin Firayim Ministan da yake da matsuguni a Rue De la Loi da ake yin taron ‘yan majalisarsa a wajen, wanda tuni yake cikin wuraren da aka kafa tsauraran matakan tsaron da aka karfafa tun bayan harin da aka kai birnin Paris.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG