SOKOTO, NIGERIA - Mawuyacin halin da ‘yan gudun hijira ke zaune ciki a Najeriya, yana kawo koma baya ga kokarin tabbatar da lafiya ga kowa cikin sauki da mahukunta ke fafatuka.
Duk da irin kokarin da hukumomi na duniya da ma gwamnatoci ke yi wajen kula da lafiya da kuma walwalar jama'a, akan samu yawaitar yanayin da ke yin barazana ga kokarin, wanda kuma kan iya kawo barkewar curutuka cikin hanzari.
Yanayin da ‘yan gudun hijira ke ciki a Najeriya na daya daga cikin abubuwanda ke kawo cututuka kuma koda yaushe sai karuruwa suke yi, sannan sun shafe lokaci mai tsawo wuri daya, ga kuma bukatu.
Wasu ‘yan gudun hijira dake Sakkwato sun bayyana cewa sun shafe shekatu har uku zaune wuri daya babu abinci mai kyau, babu sutura kuma babu matsugunni mai kyau.
Masana kiyon lafiya na ganin cewa zama cikin irin wannan yanayin tamkar jefa kai ne ga kamuwa da yada cututuka.
Dokta Awwal Ahmad Musa na ganin cewa akwai barazana sosai ga yadda zaman ‘yan gudun hijira yake yanzu a kasar, musamman duba da yanayin da suke ciki na rashi. Likitan wanda a kwanan baya ya jagoranci wani shiri na kula da lafiya kyauta a rashin tsabta, rashin ruwa rashin abinci mai gina jiki. Ya ce hakama wani aikin kula lafiyar ‘yan gudun hijira da suka yi a baya ya nuna cewa da yawa yara sun kamu da cututuka kuma sun basu magani kyauta wasu kuma an tura su asibiti.
Ko bayan abinda ya shafi kiyon lafiyar ‘yan gudun hijira, akwai bukatar abubuwan more rayuwa wanda masana ke ganin akwai bukatar mahukunta su mayar da hankali gare su, kar a yi kitso da kwarkwata domin ba'a san irin matsalar da rashin kulawa da su kan iya haifarwa ba nan gaba.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammmad Nasir: