An tabbatar da mutuwar mutane akalla 23 sakamakon ambaliyar ruwa da ta janyo bullar cutar amai da gudawa wato kwalara a cikin sansanin ‘yan gudun hijira na Minawao da ke arewancin kasar Kamaru daf da iyaka da Najeriya.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matukar damuwa a game da halin da ake ciki a wannan sansani da ke kunshe da dubban ‘yan gudun hijira mafi yawansu ‘yan Najeriya ne da suka tsere wa rikicin Boko haram.
Wani marar lafiya da ya nemi a sakaye sunansa ya ce “Ni na kawo ‘yata a yayin da na lura tana gudawa da bai tsayawa. Daga shiga wurin likita ni ma aka yi min gwaji, sai aka ce ni ma na kamu da cutar. Ga ni ga ‘yata amma jiki da sauki.”
Wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun sanar cewa fararen hula da dama na cikin mawuyacin hali a asibitoci.
Hukumomin kasar Kamaru sun yi wani taron gaggawa a ranar Laraba da ta gabata, inda suka ba da umarnin tura ma’aikatan agaji zuwa asibitoci masu cunkoso, ciki har da kan iyaka da Najeriya.
Wasu ma’aikatan agaji masu zaman kansu suna taimakawa kamar yadda shugabansu Gibaye ya ce “muna da ma’aikata da dama da muka tura su wurare daban daban. Mun hada da maikatan lafiya a gundumomi da yawa domin kawo agaji dangane da wannan annobar ."
A cewar gwamnatin Kamaru, adadin masu kamuwa da cutar na iya karuwa saboda wahalar shiga yankunan da lamarin ya shafa.
Rashin tsaro sakamakon hare-haren ta'addanci na Boko Haram na hana jami'an agaji taimakawa wadanda ake zargin sun kamu da cutar a wasu wurare da ke kan iyakar Kamaru da Chadi da Najeriya. Yankin Mayo-Sava shi ne ya fi fama da wannan annoba.
Saurari cikakken rahotan Mohamed bachir Ladan: